in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ki yarda da ziyarar shugaban Indiya a yankin da kasashen 2 suke takkadama a kai
2017-11-20 19:54:11 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin ba ta amince da kasancewar jihar Arunachal ba, sakamakon haka, ba ta amince da ziyarar shugaban kasar Indiya Ram Nath Kovind a yankin Arunachal wanda kasashen biyu ke takaddama a kan shi ba.

A kwanan baya ne dai shugaban kasar Indiyan ya ziyarci yankin da ke kan iyakar kasashen 2.

Mr Lu ya ce kafin sassan biyu su kai ga warware takkadamar, kamata ya yi su hada kansu wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kan iyakar tasu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China