Taron na yini 2 da ya gudana a hedkwatar AU dake birnin Addis Ababa na Habasha, ya amince da nazari tare da sauya tsarin tarayyar ta hanyar karawa hukumar kula da ayyukan AU karfi da inganci, bisa sanya tsarin bin bahasin ci gaban kasashen Afirka karkashin kungiyar na APRM, cikin tsarin tarayyar.
A cewar shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat, karfafa ayyukan tarayyar da kuma batun samar da kudaden ayyukanta da kanta, su ne jigon sauyin.
A wani bangare na sauyin tsarin, taron da aka kammala ya yanke shawarar rage adadin jami'an hukumar AU zuwa 8.
Har ila yau, taron ya bullo da sanya takunkumi kan mambobin da suka gaza bada kason gudunmuwarsu na shekara ga kungiyar. (Fa'iza Mustapha)