Shugaba Buhari ya ce ragin da aka samu a kasafin na shekara mai zuwa, na da nufin rage gibi, da ma yawan bashin da kasar ke karba a matsakaicin lokaci.
Kamfanin dillancin labarai na kasar NAN ya bayyana cewa, kasar na fatan rage gibin kasafin ta zuwa naira tirilin 1.86 kimanin kaso 1.3 bisa dari na GDPn kasar a shekarar ta 2019, daga Naira tiriliyan 1.95 a shekarar nan ta 2018,
Gabatar da wannan kasafin kudi na shekarar 2019, shi ne batu mafi muhimmanci da aka tsara gudanarwa a gwamnatance, gabanin babban zaben kasar na farkon shekarar 2019 dake tafe.
Yayin gabatar da kasafin, shugaban Najeriyar ya bukaci 'yan majalisun dokokin kasar da su gaggauta amincewa da shi, domin ci gaba da aiwatar da muhimman ayyuka yadda ya kamata. (Saminu)