in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan bindiga sun hallaka tsohon babban hafsan sojojin Najeriya
2018-12-20 09:51:20 cri
Rundunar sojojin Najeriya ta ce wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun harbe tsohon babban hafsan sojojin kasar Alex Badeh, yayin da yake kan hanyar sa ta komawa birnin Abuja fadar mulkin kasar.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun hallaka Mr. Badeh ne da daren ranar Talata, bayan da suka tare motar da yake ciki suka kuma bude masa wuta.

Badeh, ya taba rike mukamin babban hafsan hafsoshin Najeriya, da mukamin babban hafsan rundunar sojojin saman kasar.

Cikin wasu sakwanni da kakakin rundunar sojojin saman Najeriya Ibikunle Daramola ya wallafa a shafin sa na tweeter, ya ce marigayin na dawowa daga gonar sa ne, lokacin da maharan suka tare shi a hanyar Keffi zuwa Abuja inda kuma suka harbe shi da bindiga.

Wata majiya ta ce maharan sun kuma hallaka wasu mutanen biyu baya ga Mr. Badeh. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China