Hukumar sojin ta sauya tunaninta ne bayan wani taron ganawa da ta gudanar da masu ruwa da tsaki da kuma wasu muhimman mutane a Najeriyar, Onyema Nwachukwu, shi ne kakakin rundunar sojojin kasar ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Asabar.
Rundunar sojojin ta zargi hukumar da yin zagon kasa kan ayyukan da sojojin suke yi a yankin na kakkabe ayyukan ta'addanci da 'yan tada kayar baya a shiyyar," inda a ranar Juma'a ta ayyana janyewa daga matsayin da ta dauka a baya na haramtawa hukumar UNICEF gudanar da ayyukanta a shiyyar arewa maso gabashin kasar har na tsawon watanni 3, yankin wanda rikicin mayakan Boko Haram ya illata.
A cewar wasu bayanai na baya bayan nan, sojojin Najeriya sun gudanar da wani taron ganawa ne da wakilan hukumar ta UNICEF da yammacin ranar Juma'a.
A lokacin ganawar, sojojin sun shawarci wakilan hukumar da su guji aikata duk wani abu da zai iya haifar da koma baya wajen tattabar da tsaro a yankin, kana su nisanci yin kafar ungulu game da yakin da dakarun sojojin suke yi da ayyukan ta'addanci da masu tada kayar baya a yankin, in ji sanarwar. (Ahmad Fagam)