Tawagar kasar Sin ta bayyanawa kafofin watsa labarai cewa, a kasar Sin, babu wata doka ko daya da ta tilastawa kamfanonin kasashen waje su yi musanyar fasahohinsu. Bangarori biyu dake yin hadin-gwiwa da juna suna gudanar da musayar fasahohi ko kuma hadin-gwiwar fasahohi ne daidai wa daida bisa tushen samun moriyar juna, al'amarin da gwamnati ba za ta tsoma baki a ciki ba.
Tawagar kasar Sin ta kuma ce, kasar Sin ta yi kira da a daidaita sabanin ra'ayin kasuwancin kasa da kasa bisa tushen girmama juna gami da ka'idojin WTO.(Murtala Zhang)