in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a ba dangantaka tsakanin kasa da kasa dama
2018-09-24 14:37:27 cri
Shugaban Tarayyar Turai Jean-Claude Junker, ya ce ya kamata a ba dangantaka tsakanin kasa da aksa dama, domin ita ce hanyar samun kyakkyawar makoma.

Jean-Claude Junker wanda ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce ba sa kaunar daukar mataki na kashin kai.

Shugaban na Tarayyar Turai wanda ke a birnin New York domin halartar taron manyan jami'an kasashe mambobin MDD, ya ce wasu kasashe mamabobin majalisar na aiwatar da irin ra'ayin, sai dai, bai kira sunan Amurka ba.

Ya kuma jaddada goyon bayan Tarayyar Turai ga MDD wadda ya bayyana a matsayin tubalin kulla dangantaka tsakanin kasa da kasa.

Cikin kasa da shekaru 2, gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump, ta janye daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta duniya da hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al'adu na MDD wato UNESCO da kuma hukumar kare hakkin dan adam ta MDD. Haka zalika, ta janye tallafin da take ba hukumar MDD mai kula da rayuwar 'yan gudun hijirar Falasdinu sama da miliyan 5.

A cewar Antonio Guterres, damuwar dukkan al'ummar duniya iri guda ce, saboda dangantakar dake tsakaninsu da kuma dokokin kasa da kasa.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China