in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU ta amince da daftarin yarjejeniyar ficewar Burtaniya daga kungiyar ta gabatar mata
2018-11-26 10:32:21 cri
A jiya ne wani taron koli na musamman na kungiyar tarayyar Turai (EU) ya amince da daftarin yarjejeniyar ficewar Burtaniya daga kungiyar.

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar ta EU Jean-Claude Juncker ya bayyana cewa, shugabanni 27 sun amince da yarjejeniyar da kasar Burtaniya ta gabatar mai dauke da kusan shafuka 585 game da ficewarta daga kungiyar.

Sai dai kuma Mr Juncker ya gargadi 'yan majalisar dokokin kasar Burtaniya cewa, idan fa suka kada kuri'ar kin amincewa da wannan daftari a wata mai zuwa, to kuwa ba su samu wata yarjejeniya da ta dara wannan kyau ba.

A nata jawabin Firaministan kasar Burtaniya Madam Theresa May, ta ce 'yan majalisar dokokin Burtaniyar suna da zabi tsakanin kyakkyawar makoma da kuma rarrabuwar kawuna da ma rashin tabbas. Amma kuma 'yan adawa na cewa, Madam May za ta yi kokarin neman goyon bayan 'yan kasar yayin da majalisar dokokin kasar za ta zauna a ranar 10 ga watan Disamba, domin yanke shawarar game da ficewar Burtaniyar daga kungiyar ta EU a cikin watan Maris mai zuwa ba tare da wata yarjejeniyar ba.

Shugaban kungiyar EU Donal Tusk, ya shaidawa taron manema labarai a birnin Brussels cewa, EU da Burtaniya za su ci gaba da zama abokai har zuwa karshen kwanakin ficewarta daga kungiyar da kuma karin kwana guda.

A yau ne ake sa ran Madam May za ta yiwa majalisar dokoki jawabi, inda take fatan samun goyon bayansu kan wannan yarjejeniya. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China