Fadia Al-Barghathi, ya ce biyu daga cikin mutanen da suka jikkata na cikin yanayi mai tsanani, to sai dai kuma har yanzu mahukuntan birnin ba su fitar da sanarwa game da fashewar a hukunce ba.
Birnin Benghazi, wanda shi ne birnin na biyu mafi girma a kasar Libya, ya sha fama da makamantan wannan fashe fashe a yankunan fararen hula, ciki hadda masallatai da kasuwanni. Kaza lika masu kaddamar da harin kunar bakin wake na kaddamar da hare hare, a tashoshin binciken ababen hawa dake sassan birnin. (Saminu)