in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya na da niyyar fitar da amfanin gonarta zuwa kasar Sin ta hanyar halartar bikin CIIE
2018-12-19 14:35:47 cri

A watan Nuwambar shekara ta 2018, aka yi bikin baje-kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko a Shanghai, ko kuma CIIE a takaice, wanda ya samu halartar kasashen Afirka da dama, ciki har da kasar Kenya dake gabashin nahiyar Afirka.

CIIE ya zama tamkar wata gada tsakanin Kenya da masu sayayyar kasar Sin, musamman akwai wasu nau'o'in amfanin gonarta wadanda ke son shiga cikin kasuwannin kasar ta Sin, ciki har da furanni, da kofi da ganyen shayi, da mangwaro, da dangin gyada da sauransu.

He Qinwen, wani dan kasuwan kasar Sin ne dake ciniki a Kenya, wanda ya halarci bikin CIIE a watan Nuwambar bana a birnin Shanghai, inda ya bayyana cewa, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya zama shugaba daya tak daga kasashen kudu da hamadar Sahara, wanda ya halarci bikin CIIE, har ya yi tallar rumfar kasarsa ga mahalarta bikin, abun da ya sa rumfar Kenya ta zama daya daga cikin dakunan nune-nunen da suka fi samun karbuwa da maraba a wajen bikin CIIE.

A ganin He Qinwen, a halin yanzu masu sayayyar kasar Sin ba su san kayayyaki daga Kenya sosai ba, inda ya ce:

"Me ya sa rumfar Kenya take da farin-jini da samun karbuwa sosai a wajen bikin CIIE? Akwai mutane da dama wadanda suka taru a wajen rumfar a kowace rana, kuma da yawa daga cikinsu sun ce, suna so su dandana kofi da ganyen shayi wato "Tea" daga Kenya, da kuma dangin gyada. Har wa yau, an kawata rumfar da furanni kala-kala daga Kenya. Haka kuma an yi nunin wasu kayayyakin hannu na gargajiya na kasar, wadanda ke da ban sha'awa."

Tattalin arzikin kasar Kenya na dogaro kan ayyukan gona da kuma sana'ar yawon bude ido, kuma tana fitar da abun shayi gami da furanni masu tarin yawa zuwa kasashen Turai. A 'yan shekarun nan, kasar Sin ta zama babbar kasuwar dake shigowa da furanni daga Kenya, har ma da sauran wasu nau'ikan amfanin gona ciki har da mangwaro, da dangin gyada wadanda ke da niyyar shiga kasuwannin kasar Sin.

A nasa bangaren, Mista Brian Mchiri, wanda ya kafa kamfanin cinikin abun shayi da ake kira Home Comforts a Kenya, ya bayyana cewa, bikin CIIE ya samarwa mutanen Kenya wata kyakkyawar damar kara fahimtar kasuwannin kasar Sin, da bukatun 'yan kasuwar kasar. Mitsa Brian ya ce:

"Muna amfani da hanyoyin sadarwar zamani daban-daban don cinikin abun shayinmu. Don haka wannan dama ce mai kyau gare mu, saboda mun hadu da masu sayayyar kasar Sin da dama. Mun riga mun san me masu sayayyar kasar Sin ke so, kuma mun fahimci damammakin yin ciniki da su, shi ya sa a nan gaba, za mu kara yin mu'amala da cudanya da abokan cinikayyar kasar Sin."

Amma duk da haka, akwai sauran rina a kaba game da fitar da kayayyakin Kenya musamman amfanin gona zuwa kasar Sin. Dan kasuwa He Qinwen ya ce, Kenya ba ta da karfi sosai wajen samar da kayayyaki da kuma sarrafa su. Don haka, bayan da kasashen Sin da Kenya suka rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyin kasuwanci, ya kamata Kenya ta yi iyakacin kokarin inganta tsarin masana'antunta. Shi ma Mista Brian Mchiri, wanda ya kafa kamfanin cinikin abun shayi da ake kira Home Comforts a Kenya na ganin cewa, hadin-gwiwar da kamfanonin Kenya suka yi da kasar Sin zai taimaka musu wajen kara karfin samar da kayayyaki, inda ya ce:

"Hakan zai taimaka mana wajen daga mizaninmu. Kuma muna fuskantar wasu kalubaloli. Alal misali, yin kirkire-kirkire, da takara da sauransu. Amma mun maida su tamkar damammaki gare mu, saboda za mu iya inganta karfin kayayyakinmu wajen shiga cikin kasuwanni. Burinmu shi ne mu maida hankali sosai kan kasuwannin kasar Sin daga dukkan fannoni, kuma tabbas za mu halarci bikin CIIE na shekara mai zuwa."

Sospeter Ngoya shi ne mataimakin shugaban sashin kula da tattalin arziki, da kasuwanci na ma'aikatar harkokin wajen Kenya. Ya bayyana cewa, gudanar da bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE da kasar Sin ta yi, ya bude wata babbar kofa ga kasar Kenya da ma sauran kasashen duniya, ta yadda kasashe daban-daban za su iya samun moriyar juna. Mista Ngoya ya ce:

"Bikin CIIE ya maida hankali kan shigar da kayayyakin duniya cikin kasar Sin, wanda ya zama wani dandalin hadin-gwiwa tsakanin kasa da kasa. Bikin ya kuma samar da alheri ga duk fadin duniya, da taimakawa ga dunkular tattalin arzikin duniya baki daya. Don haka yana da amfani sosai ga jama'ar kasashen biyu wato Sin da Kenya."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China