in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mazauna kauye a Kenya suna jin dadin rayuwa saboda kama shirye-shiryen talebijin ta tauraron dan Adam
2018-08-09 14:28:35 cri

Yayin taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da ya gudana a watan Disamba na shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da daga matsayin dangantakar Sin da Afrika zuwa dangantakar hadin kai ta abota bisa manyan tsare-tsare a dukkanin fannoni, kuma ya gabatar da shirin hadin kai guda goma, dake shafar fannin masana'antu, aikin noma na zamani, ababen more rayuwa, hada-hadar kudi, samun bunkasuwa tare da kiyaye muhalli, ciniki da zuba jari cikin sauri, rage talauci, kiwon lafiya, al'adu, zaman lafiya da tsaro da dai sauransu. Wadannan shirye-shirye sun shata wata taswirar kara inganta hadin kan Sin da Afrika nan gaba, kuma ya bude wani sabon babi na sabuwar dantantakar bangarorin biyu.

Aikin samar da na'urorin kama shirye-shiryen talabijin ta taurorin dan-Adam ga mazauna kauyen na Kenya na daya daga cikin wadannan ayyuka.

Kauyen Likii, yana arewa maso yammacin tsaunin lambun shan iska dake tsakiyar kasar Kenya, kana wuri mai kayatarwa da ni'ima. Amma saboda nisansa da kuma karancin ababen more rayuwa, mazauna kauyen sun dade ba sa kallo shirye-shiryen talabijin. Dagacin kauyen Nturukuma Joseph Runyenje Lopeyok ya yi tunani cewa:

"A da ma, ba a kallon shirye-shiryen telibijin sosai, a wani wurin gidaje biyu ne ke amfani da na'urar kama shirye-shiryen talabijin daya kawai, wasu kuma ba su da telibiji din, hakan ya sa ba sa samun abubuwan dake faruwa a waje. Yara kuma su kan je gidajen makwabta masu talabijin domin su kalli shirye-shiryen telibijin a wasu lokutan ma har ba sa dawowa gida."

A shekarar 2015, shugaba Xi ya gabatar da cewa, Sin za ta samarwa kauyuka dubu 10 na'urorin kama shirye-shiryen telibiji na zamani wanda ke cikin shirye-shiryen hadin kai guda goma da ya gabatar. A ran 7 ga watan Yunin bana, kamfinin Star Times na kasar Sin ya kaddamar da wannan aiki a kasar Kenya, inda zai samarwa kauyuka 800 a kasar na'urorin kama shirye-shiryen telibijin. Garin Likki na daya daga cikin wadannan kauyuka.

Manajan huldar jama'a na kamfanin Star Times Alex Mwaura ya yi bayani cewa, wannan aiki ya samarwa mazauna kauyen Likki na'urorin kama shirye-shiryen Telibijin kyauta, wannan labari ne dadin ji ga mazauna kauyen da ba su da wadata. Ya ce:

"Mun samarwa iyalan kauyen 20 wadannan na'urori kyauta, yanzu suna iya kallo shirye-shiryen TV kyauta na tsawon wata daya, daga baya kuma za su iya kama shirye-shiryen telibijin 35 bayan da suka biyan shilling 450 a ko wane wata, idan kuma ba sa son su biyan kudi, za su iya kallon shirye-shiryen ta hanyoyi uku, wato KBC Guide Channel da CGTN."

A cewar dagacin kauyen Mista Lopeyok, zuwan wannan aiki a garinsa, ba ma kawai ya samarwa garin Likki sakon TV ba, hatta ma ya bude wata kafa ga mazauna kauyen kan yadda za su kara fahimtar abubuwan dake faruwa a duniya, da rage gibin ababan more rayuwa dake tsakanin garuruwa da birane. Ya ce:

"Na'urar kama shirye-shiryen telibijin din tana taimakawa mazauna kauyen kara fahimtar sabbin manufofin gwamnati da yadda aka aiwatar da su, alal misali, muna ganin yadda rukunin matasa masu ba da taimako na Kenya suke gudanar da aikinsu, da kuma manufar daukar renon yaro da gwamnatin ta gabatar a kwanakin baya-baya, ni da mazauna kauye mun tattauna kan wannan manufa, inda na yi musu bayani kan ayoyin dokar dake da nasaba da wannan batu."

Mazauna kauyen dake zuwa wasannin motsa jiki a cikin gari, da ma sun dogaro da rediyo don samun labarai, yanzu suna iya kallon wasanni ta telibijin dake da murya mai inganci, matakin da ya amfanawa jama'a kwarai da gaske. Lopeyok ya ce:

"Yayin da nake magana kan wannan aiki da mazauna kauyenmu, sun nuna farin ciki sosai, saboda a matsayinsu na masu kaunar kwallon kafa, suna iya kallo TV da ma wasanni daban-daban ciki hadda gasar cin kofin duniya."

Ban da wannan kuma, wannan aiki ya samarwa mazauna kauyen guraben aikin yi da dama. Alex Mwaura ya bayyana cewa, Star Times ya horar da ma'aikata a fannin gyare-gyare, don tabbatar da ganin suna kallon shirye-shirye da murya mai inganci. Ya ce:

"Mun horar da ma'aikata a fannin gyare-gyare biyu a ko wane kauye don su tabbatar da ingancin hoto da sautin shiryen-shiryen telibijin. Wannan aiki ya shafi kauyuka 800, ya kuma samar da guraben aikin yi 1600."

Ya zuwa yanzu, an kammala wannan aiki a kauyukan dake karkashin biranen Nanyuki, Isiolo, Kajiado da Nairobi, kuma ana kokarin gudanar da wannan aiki a sauran kauyuka, ana sa ran kammala wadannan ayyuka kafin watan Oktoba na bana. Alex Mwaura ya ce:

"Iyalan kauyuka 16000 da hukumomin jama'a 2400 ne za su ci gajiyar wannan aiki. Wadannan hukumomi kuma suna bautawa jama'a ne, saboda haka ina da imanin cewa, jama'a dake amfani da wannan aiki ba ma kawai na cikin wadannan kauyuka 800 ba. Ina fatan za a iya ci gaba da wannan aiki don karin mazauna kauye sun samu damar kallon labarai cikin lokaci da taimakawa tsoffi, iyaye da yara su samun ilmi daga shirye-shirye telibijin din da suke kallo."(Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China