in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar makomar da karfe da siminti za su gina wa Kenya
2018-08-20 14:21:55 cri

A karshen watan Disamban shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin "manyan shirye-shiryen hadin gwiwar Sin da Afirka guda goma" cikin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, shirin dake kunshe da fannoni da dama da suka hada da raya harkokin masana'antu, gina ababen more rayuwa, yin ciniki da zuba jari, kawar da talauci da kuma kiwon lafiya da dai sauransu, wanda ya bude wani sabon shafi na dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Kafin gudanar taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da za a yi a watan Satumba mai zuwa, bari mu dubi sakamakon da aka cimma cikin 'yan shekarun nan bisa shirin da shugaba Xi ya fidda. Kuma a shirinmu na yau, wakiliyarmu Maryam Yang, za ta gabatar wa masu sauraronmu wani labari mai taken "Sabuwar makomar da karfe da siminti za su gina a Kenya".

A watan Mayun shekarar bana, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya sake tattauna batun gina gidaje ba tare da kashe kudade mai yawa ba cikin wani jawabin da ya yi a fili.

"Muna son samar da gidaje masu araha a duk fadin kasa, yayin da ake samun karuwar guraben aikin yi da kuma karin kudin shiga tsakanin al'ummomin kasarmu. Kuma fatana shi ne dukkanin al'ummomin kasar Kenya wadanda suke kan matsakaicin matsayi na samun kudin shiga su sami gidaje masu inganci."

Batun gina gidaje masu araha shi ne daya daga cikin "manyan burika hudu na neman ci gaba" da shugaba Kenyatta ya fidda a ranar tunawa da 'yancin kai ta shekarar 2017, inda ya bayyana cewa, ya kamata a gina gidaje masu arha dubu dari 5 kafin shekarar 2022, ta yadda "kowa zai sami matsuguni".

1  2  3  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China