in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya: Darurruwan kauyuka za su kalli shirye-shiryen telebijin ta tauraron dan Adam
2018-06-12 11:05:06 cri

Kwanan baya ne aka shirya taron kaddamar da shirin "taimakawa kauyuka dubu 10 na Afirka kan yadda za su kalli shirye-shiryen telebijin ta tauraron dan Adam" a cibiyar taron kasa da kasa ta Kenyatta dake kasar Kenya, lamarin da ya nuna cewa, kauyuka guda 800 a Kenya za su kalli shirye-shiryen telebijin ta tauraron dan Adam kyauta.

A watan Disamban shekarar 2015, a yayin gudanar da taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanar da manyan shirye-shirye guda 10 na yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, ciki har da shirin "taimakawa kauyuka dubu 10 na Afirka kan yadda za su kalli shirye-shiryen telebijin ta tauraron dan Adam", a kokarin inganta rayuwar al'ummar Afirka ta fuskar al'adu da kuma kara yin mu'amala a tsakanin Sin da Afirka da kara fahimtar juna a tsakanin jama'ar bangarorin 2. Kamfanin Startimes yana gudanar da shirin ne a kauyuka dubu 10 da dari 1 da goma sha biyu na kasashe 25 na Afirka.

A wannan karo kauyuka dari 8 da ke yankuna guda 47 na kasar Kenya ne za su ci gajiyar shirin. Kamfanin Startimes zai samar wa hukumomin al'umma na ko wane kauye tsare-tsare guda 2, ta yadda za su kalli shirye-shiryen telebijin bisa amfani da hasken rana da kuma tsarin telebijin na zamani mai amfani da hasken rana kyauta, tare da samar da na'urorin kama shirye-shiryen telebijin ga iyalai guda 20, ta haka iyalai fiye da dubu 16 da kuma hukumomin al'umma dubu 2 da dari 4 za su kalli shirye-shiryen telebijin ta tauraron dan Adam kyauta. Shirin da za a gudanar cikin matakai biyu, zai lashe dalar Amurka miliyan 8 da dubu 427. An kiyasta cewa, za a kammala matakin farko na shirin a watan Agustan bana, inda zai shafi kauyuka guda dari 3. Sa'an nan kuma za a kammala mataki na biyu na shirin a watan Oktoban bana, inda sauran kauyuka guda dari 5 za su iya kallon shirye-shiryen telebijin ta hanyar tauraron dan Adam kyauta.

Ya zuwa yanzu yawancin al'ummar kasar ta Kenya suna samun bayanai game da abubuwa da gwamnati ke gudanarwa ta hanyoyin telebijin da kuma rediyo. Sakamakon kammala aikin sauya tsohon salon sadarwa zuwa na zamani da kuma habaka yin amfani da telebijin na zamani a kasar ta Kenya, ya sa al'ummar kasar suna alla-alla wajen kallon shirye-shiryen telebijin, amma duk da haka mazauna yankunan karkara a Kenya ba sa kallon shirye-shiryen telebijin a lokaci da kuma kara sanin abubuwan dake faruwa a sassan duniya ba tukuna sakamakon rashin ababen more rayuwar jama'a masu inganci da kuma kudin shigarsu. Amma yanzu shirin "taimakawa kauyuka dubu 10 na Afirka ta yadda za su kalli shirye-shirye telebijin ta tauraron dan Adam" ya kawo musu fatan alheri. Joe Mucheru, ministan sadarwa da fasaha na Kenya ya bayyana cewa, kullum gwamnatin Kenya tana girmama da kuma himmantuwa wajen kiyeya hakkin jama'arta na samun bayanai. Aiwatar da shirin "taimakawa kauyuka dubu 10 na Afirka su kalli shirye-shiryen telebijin ta hanyar tauraron dan Adam" yana taimakawa al'ummar Kenya, musamman ma wadanda suke zaune a yankunan karkara, ta yadda za su san hakkinsu, tare da taimaka musu kara sanin abubuwan dake faruwa a duniya. Jami'in ya kara da cewa, ma'aikatarsa za ta hada kai da hukumomin kasar wajen taimaka wa gwamnatin Sin da kamfanonin Sin kan aiwatar da shirin, a kokarin kawo wa jama'ar Kenya alheri.

Wasu kasashen Afirka suna fuskantar matsalar rashin ababen more rayuwar jama'a masu inganci, musamman ma rashin isasshen wutar lantarki da kuma fasaha, haka lamarin yake a kasar Kenya. Amma kamfanonin kasar Sin sun yi dabara domin daidaita wadannan kalubaloli. Zhang Junqi, shugaban reshen Kenya na kamfanin Startimes ya yi karin bayanin cewa, a yankunan karkara inda babu isasshen wutar lantarki, kamfaninsa ya yi amfani da tsarin telebijin mai amfani da hasken rana. Sun yi amfani da hasken rana ta yadda za a rika kama shirye-shiryen talabijin. Sa'an nan kuma kamfaninsa zai horas da injiniyoyin da za su rika gyare na'urorin kama shirye-shiryen a kalla 2 a ko wane kauye, inda aka kaddamar da shirin, domin saukaka al'amura, ta yadda mazauna wurin za su ji dadin kallon shirye-shiryen telebijin ba tare da wata matsala ba. An kiyasta cewa, mazauna wurin dubu 1 da dari 6 ne za su samu aikin yi. Yanzu haka masana dari 1 da 30 na wurin ne suke samun horo. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China