in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da bikin baje kolin hadin gwiwa na kayayyakin masana'antu Sin da Kenya na shekarar 2018
2018-11-16 17:21:00 cri

A ranar Laraba 14 ga wata ne, aka kaddamar da bikin baje kolin hadin gwiwa na kayayyakin masana'antu na Sin da Kenya na shekarar 2018 a birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya. A yayin wannan bikin na kwanaki hudu, wanda hukumar raya cinikayyar kasa da kasa ta Sin da Asusun ci gaban Sin da Afirka suka shirya tare, za a nuna fasahohi da kayayyaki masu inganci na Sin, domin biyan bukatun ci gaban kasar Kenya, da kuma samar da dandali ga hadin gwiwar Sin da Kenya a fannin tattalin arziki da cinikayya.

A ranar 14 ga wata ne, aka kaddamar da bikin baje kolin hadin gwiwa na kayayyakin masana'antu na Sin da Kenya a cibiyar taro ta kasa da kasa ta Kenyatta da ke birnin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya. Bikin da ya samu halartar kamfanoni 81 daga larduna da birane 15 na kasar Sin, fadin wurin bikin kuwa ya kai murabba'in mita 4300. An shirya bikin ne domin inganta hadin gwiwar kayayyakin masana'antu da kirkire-kirkiren na'urori, a kokarin kyautata matsayin Kenya na raya kanta. Kayayyakin da aka nuna a yayin bikin sun shafi fasahohin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin nukiliya, da na'urorin injiniya, da na sarrafa amfanin gona, da kuma kayayyakin mota.

Wannan shi ne karo na biyu da Rukunin raya masana'antu bisa karfin nukiliya na kasar Sin ya halarci bikin baje kolin. Yao Hong, mataimakin manajan kula da kasuwannin Afirka na rukunin yana ganin cewa, Kenya na da karfin raya fasahohin nukiliya musamman ma a fannin samar da wutar lantarki. A wannan karo, rukuninsa ya kawo sabbin fasahohi, ta yadda zai ilimantar da jama'ar Kenya a wannan fanni, tare da neman yin hadin gwiwa da hukumomi da kamfanonin kasar. Yao Hong ya kara da cewa,

"Kenya tana samun wutar lantarki ne ta hanyoyi uku, wato ruwa mai zafi da aka samu daga karkashin kasa, da karfin ruwa, da kuma kwal. Akwai rashin tabbas ga hanyoyi biyu na gaba, sannan kona kwal zai gurbata muhalli sosai. Amma game da hanyar amfani da karfin nukiliya, baya ga samar da wutar lantarki yadda ya kamata, ba za kuma a fitar da abubuwa masu gurbata muhalli ba. Don haka samar da wutar lantarki bisa karfin nukiliya wani zabi ne mai kyau sosai ga Kenya."

Ban da wannan, wani abu na daban da ya jawo hankali mutane sosai a yayin bikin shi ne rumfar nuna yankin musamman na tattalin arziki na Kogin Zhujiang na Kenya. Yankin yana garin Eldoret, an kuma kaddamar da gina shi ne a shekarar 2017 bisa hadin gwiwar Rukunin New South na lardin Guangdong na Sin da gwanmatin kenya, da niyyar raya yankin cinika maras shinge ta hanyar koyon fasahohin Sin na raya yankunan masana'antu, ta yadda Kenya za ta samu bunkasuwa a fannin masana'antu. Ko shakka babu wannan tamkar karfafawa Kenya gwiwa ne wadda ke alla-alla wajen raya masana'antunta. Peng Xiliang, mai ba da taimako ga babban manaja na kamfanin zuba jari na Rukunin New South ya bayyana cewa, Yankin musamman na tattalin arziki na Kogin Zhujiang wani abin koyi ne na hadin gwiwar Sin da Kenya ta fuskar raya masana'antu. Yana mai cewa,

"Muna amfani da fasahohi da kudade na kasar Sin, sannan muna hada wasu albarkatu tare domin gina yankin. Kenya wata babbar kasa ce wajen shigo da kaya daga ketare, ganin yadda sana'ar masana'antunta ba ta samu ci gaba sosai ba. Makasudinmu na gina yankin shi ne samar da kaya da sayar da su a kasar, a maimakon dogaro da shigo da kayan daga ketare. Har ma za a iya sayar da kayayyaki kirar Kenya zuwa kasuwannin Turai da Amurka da na Sin."

A yayin bikin, dimbin 'yan kasuwa suna ta zuwa rumfar nuna yankin tattalin arzikin. 

Madam Lilian da ke gudanar da aikin sayar da amfanin gona tana daya daga cikinsu. Ta tambayi ka'idoji da manufofin yankin domin neman samun damar raya aikinta a yankin. Ta ce, 

"Yankin masana'antun zai samar da wani kyakkyawan tsari ga 'yan kasuwa. Kamar ni, ina sayar da amfanin gona, idan zan sayar da su bayan na sarrafa su, to farashinsu zai karu. Tsarin na da ban sha'awa, kuma ba a taba ganin irinsa a Kenya ba. Bugu da kari, za a samar da muhimman ababen more rayuwa a yankin, har ma za a ba mu taimakon fasaha, lallai mu 'yan kasuwa za mu amfana sosai."

A yayin bude bikin kuwa, mashawarcin kasuwanci na ofishin jakadancin Sin da ke Kenya Guoce, da ministan masana'antu da cinikayya da hadin gwiwa na Kenya Peter Munya dukka sun bayyana fatansu ga ci gaban hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayyar Sin da Kenya, inda Guo Ce ya ce, yana fatan bangarorin biyu za su kara kiyaye kyakkyawar cudanyarsu a fannin yadda ya kamata. A nasa bangaren kuma, Mr. Munya ya ce, Kenya za ta ci gaba da kyautata yanayin zuba jari, da maraba da kamfanonin Sin wajen zubo jari a kasarta. Sa'an nan kasar za ta koyi fasahohin Sin wajen bude kofa ga waje, a kokarin raya tattalin arziki mai salon bude kofa.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China