in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummomin kasar Kenya sun ci moriya a lokacin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018
2018-07-15 17:15:27 cri

Al'ummomin kasar Kenya sun ci moriya a lokacin gasar cin kofin duniya ta wannan shekarar ta 2018 a kasar Rasha sakamakon aikin samar da tashar talabijin ta zamani da kasar Sin ta dauki nauyinsa dangane da wannan batu, abokin aikinmu Ahmad Inuwa Fagam na da karin bayani.

Joseph Runyenje Lopeyok, an haife shi ne a kauyen Likii dake kan iyakar garin Nanyuki a tsakiyar yankin Laikipia na kasar Kenya, a wancan lokacin akwai kyakkyawan misali na yawaitar munanan laifuka da yawan shan barasa.

Jami'in gudanarwar mai shekaru 50 da haihuwa, yana matukar alfahari da ya ganin irin sauye sauyen da aka samu a kauyensu musamman irin makudan jarin da aka zuba wajen samar musu da titunan mota na zamani, da ruwan sha mai tsabta, da lantarki, da makarantu da asibitoci.

Sashen gudanar da mulki na Lopeyok wanda ya kunshi kauyen Likii da kewaye sun amfana da ayyukan samarwa kauyukan Afrika dubu 10 da tashar talabijin mai tauraron dan adam wanda gwamnatin Sin da Kenya suka dauki nauyi, kuma kamfanin sadarwa na StarTimes ne ya aiwatar da aikin.

Mutumin mai 'ya'ya biyar, yana cike da annashuwa a wannan makon, a lokacin da yake bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua yadda aikin samar da na'urar kama tashoshin talabijin ta StarTimes ya canza musu rayuwa tun daga lokacin da ya fara bibiyar abubuwan dake faruwa a sassan duniya, da kuma yadda ya fara kallon gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 ta FIFA ba tare da katsewa ba.

"A koda yaushe ina sha'awar wasannin kwallon kafa, kuma StarTimes ta kashe mana kishirwar da muka dade muna jinta saboda samun damar kallon wasannin cin kofin duniya saboda yadda muke kallon hotuna da kuma sauti masu inganci kuma babu farfari," Lopeyok ya fadawa Xinhua a wata hira da ya yi kwanan nan.

Matsakaiciyar akwatin talabijin dinsa tana iya kamo tashoshi barkatai wanda kamfanin StarTimes ya samar musu domin sanin abubuwan dake faruwa a sassan duniya, da kuma irin ci gaban da ake samu a duniyar wasannin da fasahohi.

Mai sha'awar wasannin ya ce, samun damar kallon gasar cin kofin duniya ya kasance wani muhimmin al'amari mai faranta rai, godiya ta tabbatar ga kamfanin sadarwa na StarTimes sakamakon samar musu da na'urar kama tashoshin talabijin a cikin harabar gidajensu.

Yana daga cikin magidanta 20 a kauyen Likii wadanda aka zabe su domin cin gajiyar aikin samar da tashar talabijin ta zamani da kasar Sin ta samar da nufin baiwa al'ummar dama wajen ilmantarwa da nishadantarwa ga al'ummar mazauna karkara a kasar Kenya.

An kaddamar da aikin ne a farkon watan Yuni, aikin na kasar Kenya wanda kasar Sin ta dauki nauyinsa da nufin samarwa kauyuka 800 tashoshin talabijin na zamani kuma kamfanin StarTimes ya kuduri aniyar samar da na'urar kama tashar talabijin mai tauraron dan adam kimanin 18,400 ga gidaje da kuma cibiyoyin gwamnati nan da karshen watan Nuwamban bana tun bayan kaddamar da fara aikin.

Gwamnatin kasar Sin ta riga ta samar da kudaden aiwatar da shirin wanda ake burin hadawa ga magidanta 16,000 a kauyuka 800 dake fadin kasar Kenya tashar talabijin mai tauraron dan adam, kana za'a hada ma'aikatun gwamnati kimanin 2,400 da tashar talabijin mai tauraron dan Adam tare da akwatin talabijin mai girman inci 32.

A kauyen Likii mai fama da hada hada, kamfanin sadarwa na StarTimes ya makala sabbin na'urorin kama tashoshi a saman rufin gidaje ga mutane masu karamin karfin mazauna kauyen wadanda rashin karfin tattalin arziki ya hana su ikon mallakarsu, inda suke ci gaba da yin amfani da tsoffin na'uron talabijin irin na da.

Mercy Wanjiru, wata 'yar kasuwa mai shekaru 63 a duniya ta tabbatar da cewa, kamfanin sadarwa na StarTimes ya kara armashi wajen samun labarai na cikin gida, da nishadantarwa, da wasanni da kuma shirye shiryen kasashen ketare kamar shirin nan na wasan Kung Fu.

"Mun sha fama da matsalar rashin kyawun yanayin kama tashoshi kafin zuwan StarTimes ta kawo mana dauki. Ina sha'awar kallon shirye shiyen harsuna a tashoshin talabijin, kuma a halin yanzu ina iya kallon fina finai na Kung Fu wadanda suna matukar kayatar da ni," in ji Wanjiru.

"A lokacin baya, sam ban damu da kallon wasan kwallon kafa ba, amma a yanzu ina bibiyar yadda wasannin gasar cin kofin duniya ke gudana. Ina ci gaba da kallon gasar cin kofin duniya cikin zumudi," in ji ta. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China