Masanin ya ce, bai kamata Amurka ta yi kokarin jan hankalin nahiyar ta Afirka ta hanyar shafawa kasaashen Sin da Rasha kashin kaji ba.
Kalaman masanin dai na zuwa ne yayin da Amurka ta fitar da sabbin manufofinta kan nahiyar Afirka a ranar Jumma'ar da ta gabata, inda mai baiwa shugaba Donald Trump na Amurka shawara kan harkokin tsaro John Bolton ke cewa, gwamnatin Trump tana shirin yin gogayya kan yadda kasashen Sin da Rasha ke kara fadada tasirinsu na tattalin arziki da siyasa a nahiyar, inda ta zargi kasashen biyu da gudanar da harkokin kasuwanci da ba su da dace ba da ma keta dokokin kasashen nahiyar.
Mwanza ya ce, babu wani sabon abu kan abin da Amurkar za ta baiwa nahiyar a cikin sabbin dabarunta, kuma yunkurin wani karin rashin tabbas ne da gwamnatin Trump ke yi kan abin da kasar Sin ke yi a nahiyar na Afirka. (Ibrahim Yaya)