Ministan harkokin cikin gidan kasar Stephen Kampyongo wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, ya ce yanzu haka an dauki matakan da suka dace kamar yadda hukumomin lafiyar kasar suka tanada domin hana yaduwar cutar da ake dauka ta ruwa zuwa gidajen kurkukun kasar.
Ministan ya kuma shaidawa taron manema labarai cewa, daga yanzu hukumomin kula da gidajen yari ba za su bari a rika shigo da abinci daga waje zuwa cibiyoyin tsare jama'a ba. Haka kuma an haramta zirga-zirgar fursunoni da ma canzawa fursunoni wurin zama daga wannan gidan yari zuwa wancan.(Ibrahim)