Ministan harkokin kiwon lafiya na kasar Zambia Chitalu Chilufya ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ya zuwa yanzu, mutane 2148 ne suka kamu da cutar kwalara a kasar, yayin da mutane guda 51 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da wannan cuta. Ya ce, gwamnati za ta ci gaba da daukar matakai don hana yaduwar cutar a fadin kasar. (Maryam)