in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambia ta samu ragowar aurar da kananan yara da kashi 10
2018-01-19 09:49:24 cri
Shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu, ya bayyna cewa, kasar ta samu raguwar adadin aurar da kananan yara da kashi 10 bisa 100 a shekarar data gabata sakamakon matakai da dama da kasar ta dauka na magance yawaitar aurar da kananan yaran.

Lungu yace an samu raguwar ne saboda irin matakan da gwamnatinsa ta dauka wanda yayi daidai da tsarin jadawalin shirin matasa na kungiyar tarayyar Afrika AU tare da hadin gwiwar shirin kyautata rayuwar mata na MDD.

Shugaban na Zambiya ya nanata aniyar gwamnatinsa na marawa shirin kasa da kasa na yaki da aurar da kananan yara baya da kuma tabbatar da ganin an baiwa matasa mata damammaki iri daya da takwarorinsu maza.

Lungu yace, kasar Zambia tana marawa alummar kasa da kasa baya da nufin zuba jari ga harkokin da suka shafi cigaban matasa na nahiyar Afrika, kasancewar sune mafi yawa na adadin alummar dake nahiyar wadanda yawancinsu 'yan shekaru 25 ne zuwa kasa.

A shekaru da dama kasar Zambiya ta sha fama da matsalolin aurar da kananan yara wanda ya hada da yara mata 'yan kasa da shekaru 18, musamman a yankuna karkara na kasar dake kudancin Afrika.

Kasar itace ke sahun gaba a duniya wajen aurar da kananan yara, inda ake samun kashi 42 bisa 100 na matan 'yan shekaru 20 zuwa 24 wadanda ake aurar dasu gabanin su cika shekaru 18 da haihuwa. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China