in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan kasar Zambiya sun cafke mutane 55 a babban birnin kasar
2018-01-13 14:03:36 cri
Wani jami'in gwamnatin kasar Zambiya yace a kalla mutane 55 ne aka damke a babban birnin kasar bayan rikici da ya barke sakamakon dokar da hukumomi suka kafa na killace kasuwannin kasar a matsayin matakan kariya daga cutar kwalara wadda ta barke a kasar.

Ministan harkokin cikin gidan kasar Stephen Kampyongo, ya bayyana cewa, abu ne da ba za'a taba lamunta ba wasu mutane su dinga karya doka, wanda hakan zai iya haifar da matsala game da matakan kariya ga lafiyar jama'a duba da irin matsalar cutar kwalara da ta barke, kana gwamnatin kasar na cigaba da dakile bazuwar cutar a halin yanzu.

Hukumomin kasar sun rufe kasuwanni a babban birnin kasar, kuma sun dakatar da hada hadar kasuwanci a unguwanni tun bayan barkewar cutar kwalara wanda kawo yanzu ta yi sanadiyyar hallaka rayukan mutane 65 a babban birnin kasar.

Dakarun sojin kasar suna cigaba da kula da tsabtar yankunan kasuwancin kasar.

Bugu da kari, ministan kananan hukumomin kasar Vincent Mwale, ya bayyana cewa, gwamnati zata fara aikin bude wasu daga cikin kasuwannin babban birnin kasar wadanda suka mutunta ka'idojin da gwamnatin ta kafa.

Ya bayyana a lokacin taron manema labarai cewa, hukumomin kasar sun fito da wasu ka'idoji wadanda ya zama tilas kasuwannin kasar su cika su gabanin a basu damar sake gudanar da kasuwanci.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China