Xi ya ce, jam'iyyar kwaminis tamkar tushe ne na gudanar da harkokin kasar Sin yadda ya kamata, kuma ya kamata a tafiyar da harkokin jam'iyyar ta hanyar da ta dace kuma daga dukkanin fannoni. Xi ya ce, ya zama dole a karfafa hadin-gwiwar jam'iyyar, da kyautata shugabancinta nagari, da horas da kyawawan mahukuntan jam'iyyar, wadanda ke nuna biyayya da ladabi ga jam'iyyar kwaminis. Xi ya kuma ce, ya kamata a yi iyakacin kokarin kawar da dukkanin mutanen da suka aikata laifin cin hanci da karbar rashawa, da tabbatar da samun jami'an gwamnati masu rikon gaskiya da adalci, ta yadda za'a kirkiro wani yanayin siyasa mai tsabta, a ci gaba da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.(Murtala Zhang)