in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Gyare-gyare da bude kofa# Xi: Ba za a iya ware yanki daga kasar Sin ko kadan ba
2018-12-18 12:34:00 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau cewa, kasar Sin za ta bi manufofi masu gudanar da harkokin kansu na "kasa daya tsarin mulki iri biyu", "a bar mutanen Hong Kong su kula da harkokin kansu", "a bar mutanen Macau su kula da harkokin kansu", tare kuma da gudanar da ayyuka bisa tsarin mulkin kasa da babbar doka, da kyautata tsare-tsaren dake da nasaba da gudanarwar babbar doka, don tabbatar da zaman karko da wadata a Hong Kong da Macau cikin dogon lokaci, da nuna goyon baya da inganta ayyukan shigar da Hong Kong da Macau cikin kasar Sin yadda ya kamata, da nufin sanya 'yan uwan Hong Kong da na Macau su yi kokari tare da jama'ar babban yankin kasar Sin, don daukar nauyin dake bisa wuyansu na farfado da al'umma, da jin dadi kan wadatuwar kasar Sin.

Baya ga haka, Xi ya jaddada cewa, ya kamata a bi manufar Sin daya tak, da ra'ayi daya da aka cimma na shekarar 1992, don inganta tushen zaman lafiya na dangantakar dake tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan, da zurfafa yin mu'ammala da hadin kai a tsakanin gabobin biyu a fannonin tattalin arziki da al'adu, don samar da gajiya ga 'yan uwan gabobin biyu. A cewarsa, kasar Sin na da niyyar da karfi wajen kiyaye mulkin kai da cikakken yankin kasa, kuma ba za a iya ware ko wane yanki daga kasar ba. (Bilkisu Xin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China