in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Gyare-gyare da bude kofa# Xi: Wajibi ne kasar Sin ta tsaya kan habaka bude kofa ga kasashen ketare
2018-12-18 12:27:27 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Talata cewa, bunkasuwar kasar Sin na dogaro da duniya, kana wadatuwar duniya ma na bukatar kasar Sin. Wajibi ne kasar Sin ta tsaya kan habaka bude kofa ga kasashen ketare, da inganta kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama. Xi ya kara bayyana cewa, kasar Sin za ta yi kokarin inganta kafa sabuwar alakar kasa da kasa irin ta nuna girmama wa juna, da adalci da kuma hadin kai irin na samun nasara tare, kana da girmama hakkin jama'ar kasashe daban daban, da zaben hanyar ci gaba mai dacewa, tana ma adawa da kutsa kai cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe, da wulakanta marasa karfi. Baya ga haka, kasar Sin za ta taka rawarta bisa matsayin ta na wata babbar kasa, za ta goyi bayan kasashe masu tasowa, da sa himma wajen shiga ayyukan yin kwaskwarima da raya kan tsarin gudanar da harkokin duniya, kana tana goyon bayan tsarin cinikayya na bangarori da dama, da inganta samar da sauki ga yin cinikayya cikin 'yanci. Baya ga haka za ta dora muhimmanci sosai kan shawarar "Ziri daya da hanya daya" a yayin kokarin da take yi tare da bangarori daban daban wajen kafa sabon dandalin hadin kan kasa da kasa. (Bilkisu Xin)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China