Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana yau cewa, dole ne kasar Sin ta mai da batun neman ci gaba a gaban kome, a kokarin kara karfin takarar kasar daga dukkan fannoni. Kana dole ne a gaggauta raya tsarin tattalin arziki mai salon zamani bisa aniyar warware sabani da ke tsakanin bunkatun jama'a na dinga neman jin dadin zaman rayuwa, da matsalar rashin samun daidaito wajen bunkasuwa, a kokarin samun dauwamammen ci gaba mai inganci da alalci. Haka kuma za a canja salon bunkasuwa, da kyautata tsarin tattalin arziki, da sauya fannin da ake dogara a kai wajen neman samun karuwar tattalin arziki. Bugu da kari, za a aiwatar da mai da hankali kan kirkire-kirkire, da raya muhimman fasahohi bisa karfin kanta, domin goyon bayan ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Haka zakila ma za a dora muhimmanci kan kiyaye muhalli, da canja tsohon salon bunkasuwa da na zaman rayuwar jama'a, ta yadda jama'a za su rayu cikin muhalli mai tsabta.(Kande Gao)