in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Gyare-gyare da bude kofa# Xi: Kamata ya yi a sanya jama'a su ci gajiya daga gyare-gyare
2018-12-18 11:56:16 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yayin babban taro na murnar cika shekaru 40 da soma yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje da aka shirya a yau Talata, cewa dole ne a dora muhimmanci kan jama'a a yayin da ake gudanar da manufar ta yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, ya kamata a girmamawa ra'ayin jama'a da kula da yanayin da suke ciki, da kuma kokarin kyautata zaman rayuwarsu. Xi ya kuma nuna cewa, wajibi ne jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta mai da kyautata zaman rayuwar jama'a a matsayin burinta, da kyautata tsarin demukuradiyya, da habaka hanyar demukuradiya, da wadata hanyoyin gudanar da wannan aiki, kana da kyautata tsarin ba da tabbaci a fannin doka da oda, da nufin tabbatar da jama'a sun samu ikon demukuradiyya. Baya ga haka, ya kamata a warware matsalolin gaggawa da jama'a ke fuskanta, da taimaka masu wajen cin gajiyar nasarorin da aka samu a fannonin tattalin arziki, siyasa, al'adu da kuma hallitu da dai sauransu. (Bilkisu Xin)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China