Yau shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, idan ana son ingiza gyare-gyare da bude kofa a sabon zamanin da ake ciki, ya dace a daidaita huldar dake tsakanin gyare-gyare da raya kasa, kasar Sin tana da girma, a don haka dole ne a kaucewa kuskure kan manyan batutuwan dake shafar babbar moriyar kasa, haka kuma a yi hangen nesa, da nazari kan matsalolin da kasar take fuskantar domin neman samun matakan da za su dace, ta yadda za a daidaita matsalolin lami lafiya. shugaba Xi ya jaddada cewa, yayin da ake kokarin yin gyare-gyare, ya kamata a rika hada manufar yin gyare-gyare da matakan raya kasa cikin kwanciyar hankalli.(Jamila)