in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron MDD kan kyautata rayuwar hallitu a Masar
2018-11-18 16:02:12 cri

An bude taro na 14 na bangarorin da suka cimma yarjejeniyar kyautata rayuwar halittu, jiya Asabar a birnin Sharm El-Sheikh na Masar, inda masana daga sama da kasashe 190 suka hallara, da nufin ingantawa da kare rayuwar halittu.

Da yake gabatar da jawabin bude taron, Shugaban kasar Masar, Abdel-Fattah al-Sisi ya ce kasarsa ta dauki batun kyautata rayuwar hallitu da matukar muhimmanci domin cimma ci gaba mai dorewa. Haka zalika kudurin al'ummar kasar ne kare muhalli da albarkatu bisa koyarwar addinin da al'adunsu.

A nata bangaren, ministar muhalli ta kasar, Yasmine Fouad, ta ce taron zai yi nazarin yadda aka aiwatar da jadawalin kyautata rayuwar halittu na shekarar 2011 zuwa 2022, da kuma tsara na sauran shekarun da suka rage, tare da share fagen bullo da wanda za a aiwatar bayan shekarar 2020.

Ta ce gudanar da taron a Masar, shi ne na farko da aka yi a nahiyar Afrika tun shekarar 2000, haka zalika karon farko da aka yi a kasar Larabawa, wanda ta yi amana zai kara karfafa hadin gwiwar kare lalacewar hallitu a duniya da kuma taimakawa wajen wayar da kai game da kyautata rayuwar hallitu a yankin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China