Kotun hukunta manyan laifuffuka ta Alkahira ta kuma bada umurnin kwace dukiyoyin wadannan mutane, don kwamiti na musamman ya kula da su.
Akasarin masu tsattsauran ra'ayin Islama da masu biyayya ga manufofin kungiyar 'yan uwa musulmi ne ake tsare da su a gidan kurkuku, ko kuma gudun-hijira suke a halin yanzu, bayan da aka hambarar da tsohon shugaban kasar Masar Mohamed Morsi a farkon watan Yulin shekara ta 2013.
An yankewa Morsi hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kaso sakamakon hura mummunar wutar rikicin da ake tuhumarsa a tsakanin magoya bayansa da masu adawa da shi a karshen shekara ta 2012. Haka kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru 25 saboda ya bayar da wasu bayanan sirri ga kasar Qatar.
Bayan da aka kifar da gwamnatin Mohamed Morsi, kasar Masar ta sha fuskantar jerin hare-haren ta'addanci da dama, al'amuran da suka hallaka daruruwan 'yan sanda da sojoji gami da fararen-hula a kasar. (Murtala Zhang)