Kasashen biyu sun cimma wannan matsaya ce a jiya Lahadi bayan wata ganawa da ministan tsaron kasar Sudan Awad Ibn Aouf ya yi da takwaransa na kasar Masar Mohamed Zaki a Khartoum, babban birnin kasar Sudan.
Kamal Abdul Marouf ya ce tattaunawar sassan biyu ta yi armashi, kasashen biyu sun kuma amince su kafa ayyukan hadin gwiwa ta hanyar musayar kwasa-kwasan horas da jami'an sojojin kasashensu.
Jami'in ya kara da cewa, kasashen Sudan da Masar sun kuma amince su karfafa alakarsu a dukkan fannoni, da karfafa alaka bisa manyan tsare-tsare da kulla alakar aikin soja bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni.
A ranar Asabar din da ta gabata ce dai ministan tsaron kasar ta Masar ya isa Khartoum don gudanar da ziyayar aiki ta kwanaki biyu a kasar Sudan. (Ibrahim Yaya)