in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasuwar Afirka na kokarin fara amfani da hanyoyin zamani wajen fadada harkokinsu
2018-12-12 09:48:02 cri
'Yan kasuwar Afirka dake tashe, na yunkurin ganin sun ci gajiyar damammakin hanyoyi na zamani wajen fadada harkokinsu a sassa daban-daban na duniya.

Babbar darektar cibiyar fasahar kere-kere da kirkire-kirkire mai suna Afrilabs dake Najeriya Anna Ekeledo ce ta bayyana hakan yayin taron kolin cinikayya ta Intanet a Afirka. Tana mai cewa, jagororin shirin a nahiyar sun bayyana cewa, harkar ciniyayya ta yanar gizo za ta taimakawa 'yan kasuwar nahiyar, gano sabbin kasuwanni da kara samun hanyoyin kudaden shiga.

A jawabinsa yayin bude taron kolin, shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya karfafawa matasa 'yan kasuwa na Afirka da su yi kyakkyawar amfani da damar da fasahar zamani ta kawo wajen bunkasa harkokin cinikayya tsakanin kasashen nahiyar.

Shi ma shugaban shagon sayar da kayayyaki ta yanar gizo mai suna Jumia Afirka Nicolas Martin, ya bayyana cewa, zuba jari a bangaren fasahar zamani zai kara hafimtar da matasa da ma masu sayan kayayyaki na Afirka muhimmancin tsarin.

Martin ya ce, kamata ya yi nahiyar Afirka ta kasance nahiyar da harkokin cinikayya ta Intanet za ta bunkasa a nan gaba, duba da yadda ake amfani da Intanet da ma mallakar wayoyin hannu na zamani a nahiyar.

Taron na kwanaki biyar, wanda kasar Kenya ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyoyin AU da EU ya samu halartar ministoci, da shugabannin masana'antu, da masu kirkire-kirkire da masu bincike gami da masu ba da gudummawa. Ana kuma sa ran za su tattauna game da zakulo sabbin dabarun inganta harkokin cinikayya ta Intanet a nahiya mafi girma ta biyu a duniya. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China