in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya: Kasashen Afirka na dandana kudar sakamakon cin hanci
2018-12-11 09:07:37 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, nahiyar Afirka ta dade tana dandana kudarta, sakamakon cin hanci da ya dabaibaye nahiyar tun samun 'yancin kai.

Shugaba Buhari wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron horaswa kan yaki da cin hanci da aka shiryawa shugabanni da manyan jami'an hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kungiyar tarayyar Afirka, ya kuma yi kira ga shugabannin nahiyar Afirka da su ci gaba da bullo da manufofi da managartan tsare-tsare da za su taimaka wajen hukunta jami'an da suka yi zubda ciki da dukiyar kasa.

Ya ce, kasarsa ta riga ta dauki matakan da suka dace na magance wannan nmatsala. Ya kuma shaidawa mahalarta taron cewa, kafin ya kama aiki a watan Mayun shekarar 2015, cin hanci da rashawa sun zama ruwan dare a kasar.

Shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa tana kara daukar matakai na dawo da kima da tsarin tafiyar da harkokin gwamnati bisa doka, kana za a hukunta duk wadanda aka kama da laifin satar dukiyar al'umma. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China