in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Najeriya sun dakile yunkurin harin kunar bakin wake na 'yan Boko Haram
2018-12-14 09:32:57 cri
Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta sanar da cewa jami'anta sun yi nasarar dakatar da wata mace 'yar kunar bakin waki wacce ta yi yunkurin kutsawa shingen binciken jami'an tsaro inda ta kuduri aniyar kaddamar da harin kunar bakin waken a birnin Maiduguri dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, ana zargin matar da yi wa kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram aiki.

Matashiyar wacce abubuwan fashewar dake jikinta suka tashi da ita a daidai lokacin da ta yi yunkurin wucewa ta gaban shingen binciken da jami'an tsaron suka kafa a Maiduguri, babban birnin jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya da yammacin ranar Laraba.

Babban jami'in hukumar 'yan sandan jahar Borno, Damian Chukwu, ya fadawa manema labaru cewa, ba'a samu rahoton jikkatan koda mutum guda ba.

Chukwu ya ce, ana zargin 'yar kunar bakin waken mayakan Boko Haram ne suka aika ta. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China