Ejike Martins, jami'in hukumar ba da agajin gaggawa na kasar NEMA ya bayyana cewa, "hakikanin abin da ya faru da ginin shi ne dukkan hawan benayen sun rufta ne daya bayan daya, matsalar da aka fuskanta shi ne dole ba za'a iya zakulo gawarwakin ba sai an bi sannu a hankali," Martins ya shedawa taron manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Ginin, yana wani yanki ne wanda gwamnati ta kebe a babban birnin, wanda ake ci gaba da aikin gina shi makonni 3 da suka gabata bayan da ginin ya rufta.
Yadda masu aikin ceto suka gudanar da aikinsu ba tare da nuna kuzari ba ya haifar da cece kuce a tsakanin al'ummar yankin. (Ahmad Fagam)