in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta karyata kalaman da tsohon shugaban kasar ya yi gabanin zaben dake tafe
2018-12-11 09:26:09 cri
Mahukunta Najeriya sun karyata kalaman da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya yi gabanin zabukan kasar na shekarar 2019 dake tafe.

Da yake mayar da martani a madadin gwamnatin Najeriya jiya Litinin a Abuja, babban birnin kasar ministan watsa labaran kasar Lai Mohammed ya ce, koda yake kundin tsarin mulki ya baiwa Obasanjo 'yanci na goyon bayan duk dan takarar da yake so, ko tsayar da shi, amma ba shi da ikon ba shi tabbacin samun nasara.

Ya ce yana ga kimar Obasanjo, amma watakila na kusa da shi ba su yi masa cikakken bayani game da abubuwan dake faruwa a kasar kafin ya yi wancan kalami ba, don haka ko shakka babu dan takarar da Obasanjon ke goyon baya a zaben shugabancin kasar zai sha kaye.

An dai ruwaito Obasanjo a baya na cewa, sakarai ne kawai zai tsaya a bayan fage yana kallo, a lokacin da 'yan dagaji ke wargaza kasarsa, ga cin hanci, da rashin sanin inda aka dosa, ga matsalar tsaro da nuna bambanci da sauransu sun dabaibaye kasar. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China