in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta kudu za ta nace ga manufar raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba
2018-12-13 10:54:20 cri
Ministar kula da muhalli ta kasar Afirka ta kudu Nomvula Mokonyane ta bayyana aniyar kasarta ta ci gaba da aiwatar da ajandar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba a kasar da ma nahiyar Afirka baki daya .

Mokonyane ta bayyana hakan ne yayin da take sanar da shirin gwamnati na karbar bakuncin taron kawancen raya tattalin arzikin albarkatun ruwa (PAGE) da zai gudana tsakanin ranakun 10 da 11 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2019 a birnin Cape Town.

Taron na PAGE, yana goyon bayan kasashen da yankuna da su ba da muhimmanci ga manufofi da shirye-shiryen tattalin arziki, domin ciyar da ajandar nan ta samar da dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China