in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu ta yi kira ga BRICS da ta inganta ci gaban tattalin arziki
2018-12-05 10:54:31 cri
Shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya yi kira ga kasashen BRICS da su ci gaba da aiki don inganta ci gaba tattalin arziki da kyautata rayuwar al'umma.

Cyril Ramaphosa na wannan bayani ne ga taron jam'iyyun siyasar kasashen BRICS da wasu jam'iyyu a Pretoria. Taron ya samu halartar jami'iyyu masu mulki na kasashen Brazil da Russia da India da Sin da Afrika ta kudu da Jam'iyyun 'yantar da al'ummar Afrika da wasu jam'iyyun kawance.

A cewar Cyril Ramaphosa, dole ne jam'iyyun siyasa na kasashen BRICS su rika hangen nesa da samar da manufofi yayin da shugabannnin kasashen ke haduwa a fadin duniya. Ya ce taron zai ba jama'arsu kwarin gwiwa, don haka ya kamata su daukaka fatansu da kuma tabbatar da burin jama'ar na kyautata musu tsarin duniya.

Ya kuma bukaci shugabannin kungiyar su yi kokarin ganin an samu nasarar magance kalubalen da duniya ke fuskanta, inda ya jadadda cewa kasashen BRICS sun amince da tsarin huldar kasa da kasa da cinikayya cikin 'yanci da adalci.

Har ila yau, ya ce ya kamata a yi amfani da manufofi wajen samun ci gaba na bai daya da inganta tattaunawar da za ta kara tabbaci ga ci gaban tattalin arziki da duniya ke bukata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China