in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sashen sufuri da yawon shakatawa na iya bunkasa ci gaban Afirka, in ji jami'in WTTC
2018-11-20 10:23:26 cri
Daraktan sashen bincike na hukumar sufuri da yawon shakatawa ta kasa da kasa WTTC Rochelle Turner, ya ce idan har an inganta ayyuka yadda ya kamata, sashen sufuri da yawon bude ido na kasashen dake nahiyar Afirka, na iya samar da karin kudaden shiga da ci gaba cikin sauri.

Mr. Turner ya bayyana hakan ne, yayin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Ya ce abun da kawai ake bukata domin samun nasara shi ne, kasashen nahiyar su inganta tsarin su na samar da VISA, da kuma shigar da fasahohin zamani domin kyautata ayyuka.

Jami'in ya kara da cewa, wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, sashen sufuri da yawon shakatawa na yankin kasashen dake kudu da hamadar saharar Afirka, na iya daga mizanin tattalin arziki na GDP yankin da kaso 4.4 bisa dari a duk shekarar nan da shekarar 2028.

Ana sa ran shugabar WTTC Gloria Guevara, za ta gabatar da jawabi, ga taron shugabannin Afirka da zai gudana a birnin Stellenbosch na Afirka ta kudu a ranar Alhamis. Taron wanda zai hallara sama da masu ruwa da tsaki 100 daga ciki da wajen nahiyar, zai ba da damar tattaunawa, da cudanya, da musayar dabarun masana, da zakulo hanyoyin ci gaba.

Za kuma a tattauna game da karfafa gwiwar al'ummun nahiyar, da wanzar da ci gaba, tare da amfani da kimiyya don fadada ci gaba. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China