Ma'aikatar lafiya ta kasar Afrika ta kudu ta ce la'akari da hare-haren da ake kai wa jami'an lafiya a baya-bayan nan a wasu asibitoci a kasar, za a tura 'yan sanda su rika sintiri a wasu daga cikin asibitoci domin kiyaye tsaro.
Kakakin ma'aikatar Popo Maja, ya ce a wannan lokaci na bukukuwa, an ba su tabbacin 'yan sanda za su taimakawa wajen yin sintiri a wasu muhimman asibitoci, musammam ma a wuraren da ake fi samun riginginmu.
An kai wa likitoci 3 na asibitin Letaba dake Limpopo hari makonni kadan da suka gabata. Inda ake zargin wata tawagar masu dauke da makamai da ta ci karfin jami'an dake gadi, da raunata likitocin.
A cewar Popo Maja, su na zargin harin ya samo asali ne daga laifukan da ake aikatawa wanda ba za a lamunta ba, kuma a don haka ne 'yan sanda suka ce za su kara sintirin da suke yi. (Fa'iza Mustapha)