in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An umarci tsohon shugaban Afrika ta kudu ya biya kudin hidimar shari'ar da ake masa
2018-11-10 16:09:48 cri
Wata kotu a Afrika ta kudu, ta umarci tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, ya biya kudin hidimar shari'ar da ake masa dake da alaka da zargin amfani da karfinsa wajen cin hanci

A baya, fadar shugaban kasar ce ta ce za ta rika biyan kudin hidimar shari'ar da ake wa Zuma, har sai in kotu ce ta hana.

Shugaba Cyril Ramaphosa, ya ce tuni aka biya Rand miliyan 15.3, kwatankwacin dala miliyan 1.1, na hidimar shari'ar, inda tsohon shugaban ke fuskantar tuhumar dake da alaka da karbar cin hanci wajen ba da kwangilar sayen makamai, daga kamfanin Thales na kasar Faransa, a karshen shekarun 1990.

Haka zalika, ana tuhumar Zuma da hada baki da iyalan Gupta 'yan asalin kasar Indiya, wajen yin ruf da ciki kan dukiyar kasa, zargin da shugaba Zuma da iyalan Guptan suka musanta.

Jam'iyyar adawa ta DA ta yi maraba da wannan hukunci, tana mai cewa ba nasara ce ta jam'iyyar kadai ba, har ma da daukacin masu biyan haraji a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China