A jiya Laraba ne aka kaddamar da wannan na'ura mai karfin kilowatts 500 a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Moi dake birinn Mombasa dake gabar teku. Ana kuma fatan na'urar za ta rage a kalla tan 1,300 na hayaki mai gurbata muhalli da ke shiga sararin samaniya.
Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman kasa da kasa Olumuyima Benard Aliu, ya ce wannan wani babban ci gaba ne ga bangaren zirga-zirgar jiragen saman kasar Kenya da ma nahiyar Afirka baki daya, baya ga fa'idar da za a girba daga wannan sabon canji da aka samu.
Ana kuma sa ran nau'rar za ta samar da Kilowatts dubu 820 na hasken wutar lantarki a shekara, za kuma ta rage a kalla tan 1,300 na hayaki mai gurbata muhalli a kowace shekara. Ana kuma fatan kasashe 14 za su rungumi wannan tsari, kasashe 12 daga yankin Afirka ne sai kuma kasashe 2 daga yankin Karebiya. (Ibrahim)