in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamaru: An yi garkuwa da 'yan makaranta 15 a yakin da ake amfani da turancin Ingilishi
2018-11-21 10:53:45 cri
Mahukunta a kasar Kamaru, sun ce wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara 'yan makaranta da malaminsu su 15, daga wata makaranta mai zaman kan ta dake Kumba, a kudu maso yammacin kasar Kamaru.

Yankin kudu maso yammacin Kamaru dai ya sha fama da tashe tashen hankula, masu nasaba da yunkurin kafa kasar 'yan a ware ta Ambazonia, kuma yana cikin yankuna dake da mafi yawan masu amfani da turancin Ingilishi a kasar.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ta wayar tarho, ministan ma'aikatar watsa labarai na kasar Issa Tchiroma Bakary, ya ce gwamnati na kokarin gano yadda wannan lamari ya auku, da kuma inda 'yan bindigar suka boye yaran.

Wannan ne dai karo na biyu cikin wata guda, da masu garkuwa da mutane ke sace 'yan makaranta a yankunan dake amfani da turancin Ingilishi, inda a ranar 4 ga wata ma wasu da ba san ko su waye ba, suka yi garkuwa da 'yan wata makaranta mai zaman kan ta su 79, a yankin arewa maso yammacin kasar. Sai dai rahotanni sun ce daga bisani an sako yaran bayan 'yan kwanaki suna tsare. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China