Stephane Dujarric, ya ce ofishin MDD dake lura da 'yan gudun hijira ko OCHA, da abokan huldar sa, na kara kaimi wajen taimakawa fararen hula da rikici ya raba da muhallan su, a yankunan kudu maso yammaci da arewa maso yammacin kasar. Ya ce hukumar OCHA ta yi korafi game da karancin tsaro a yankunan biyu, da kuma karancin kudaden gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
OCHA ya ce bisa wasu rahotanni, shirin tallafi na kasar Kamaru, wanda aka yi hasashen zai lashe kudi har dalar Amurka miliyan 320, ya gamu da gibin kusan kaso 37 bisa dari, yayin da ayyukan gaggawa da aka yi hasashen za su bukaci kudi har dala miliyan 15, domin tallafawa mutane kusan 160,000, suka samu kudi da bai wuce dala miliyan 5 kacal ba.
Tun daga shekarar bara ne dai 'yan aware a kasar ta Kamaru, ke kaddamar da hare hare a yankunan dake amfani da turancin Ingilishi a yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar, a wani mataki da suka ce martani ne, bisa wariya da tsagin 'yan kasar mafiya rinjaye masu amfani da yaran Faransanci ke nuna masu. (Saminu)