Jami'an WFP, sun ce an fara rabon abincin ne ga 'yan gudun hijirar dake yankin Yamma da kuma yankin Littoral, wadanda ke kan iyakar yankunan kasar 2, na arewa maso yamma da kudu maso yamma dake da rinjayen masu amfani da Turancin Ingilishi.
Nazarin da tawagar MDD ta yi, ya nuna cewa akwai kimanin 'yan gudun hijira 78,000 a yankin yamma da kuma Littoral.
Jami'an sun ce 'yan gudun hijira 50,000 ne, za su samu agagjin abinci metric ton 1,900 a cikin kashin farko na rabon.
A cewar babban wakilin WFP a Kamaru, za su yi nazarin yadda aikin ya gudana bayan kammala kashin na farko, daga nan sai su san yadda za su ci gaba da aiwatar da shi. (Fa'iza Mustapha)