in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An saki daliban jami'ar Bamenda na kasar Kamaru 17 da aka sace
2018-12-13 09:35:27 cri
Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa, an saki daliban jami'ar Bamenda 17 da aka kama ranar 5 da kuma 10 ga watan Disamban da muke ciki.

Da yake karin haske game da sakin daliban, gwamnan yankin arewa maso yammacin kasar, daya daga cikin yankunan kasar da ke magana da turancin Ingilinshi da yaki ya wargaza, Lele Lafrique ya bayyana cewa, an yi nasarar kubutar da daliban ne, bayan wani samame da hukumomin yankin da dakarun tsaro da iyayen daliban gami da wasu 'yan kasa masu kishi dake makwabtaka da yankin suka kaddamar.

Gwamna Lele ya ce, wata kungiyar bata garfi da ta kware a satar dalibai don neman kudin fansa ne ta sace su. A farkon watan Nuwamba ma, mahukuntan kasar sun zargi 'yan aware da sace daliban wata makaranta mai zaman kanta guda 79 a yankin arewa maso yammacin kasar. Sai dai an sake su bayan wasu 'yan kwanaki, Amma kuma 'yan awaren sun tsaya kai da fata cewa, gwamnati ce ta kitsa galibin sace-sacen daliban da nufin bata musu suna a idon duniya. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China