Tchiroma ya ce, daga bisani yaran sun hadu da iyayensu.
Kakakin rundunar sojojin kasar ta Kamaru, Kanar Didier Badjeck, ya ce an saki mutane 80 da ake garkuwa da su ne a safiyar yau Laraba, bayan wani samame da sojojin suka kaddamar a Bafut, wani kauye dake wajen Bamenda,babban birnin yankin arewa maso yammacin kasar.
A ranar Lahadi da dare ne dai aka sace daliban da malamansu a yankin arewa maso yammacin kasar, daya daga cikin yankunan da ake magana da Turancin ingilishi mai fama da tashin hankali.(Ibrahim)