Issa Tchiroma, wanda kuma shi ne kakakin gwamnatin kasar, ya ce an dauki dukkan matakai daga bangarorin farar hula da soji, domin tabbatar da an dawo da daliban da malamansu cikin koshin lafiya, ya na mai cewa ana binciken tungar wadanda suka sace su.
Wata majiya daga jami'an tsaro ta shaidawa Xinhua cewa, an sace daliban da malamansu ne daga wata makarantar sakandare mai zaman kanta mai suna Presbtyterian dake yankin Nkwen na Bamenda, babban birnin yankin arewa maso yammacin kasar.
Minsitan ya ce masu satar mutanen za su nemi kudin fansa, domin shi ne dalilin mummunan aikin na su.
Wani fitattacen shugaban 'yan aware Eric Tataw, ya fitar da wani bidiyo a baya-bayan nan, wanda ya nuna dalibai 11 a tsorace, inda 'yan aware dauke da makamai ke yi musu tambayoyi. (Fa'iza Mustapha)