in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta kaddamar da dandalin cinikayyar kayayyaki
2018-11-07 11:03:29 cri
Shugaban Ghana Nana Akufo Addo, ya kaddamar da dandalin cinikayyar kayayyaki na Ghana GCX, wanda ke matsayin kasuwar saye da sayarwar amfanin gona.

Dandalin na GCX, kasuwa ce da gwamnati za ta rika tafiyar da harkokinta, wadda za ta hada masu saye da sayarwa, ta yadda za su yi cinikayya bisa dokoki, yayin da gwamnati za ta tabbatar da ingancin kayayyaki da aikewa da kayayyakin da aka saya da biyan kudadensu a kan kari.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da kasuwar, shugaba Akufo Addo, ya ce GCX za ta zama daya daga cikin jigogin tabbatar da burin gwamnatinsa, na zama cibiyar samar da amfanin gona a yammacin Afrika.

Ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kasuwar ta sauke nauyin dake wuyanta, tare da inganta samar da kayayyaki da tsayayyen farashi da kara fitar da kayayyaki da kuma rage shigar da su kasar daga ketare.

Ya kara da cewa, kasuwar wadda aka yi bisa bullowar yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar, za ta mayar da Ghana muhimmiyar cibiyar cinikayya a yankin yammacin Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China