in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe jami'ar Kwame Nkrumah sakamakon boren dalibai
2018-10-23 19:29:33 cri
Mahukunta a kasar Ghana, sun ba da umarnin rufe jami'ar koyon ilimin kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah dake birnin Kumasi, birni na biyu mafi girma a kasar, sakamakon boren dalibai, wanda ya sabbada lalata wasu gine gine, da kayan aiki a jami'ar.

Rahotanni na cewa an dauki matakin rufe jami'ar ne, bayan barkewar tashin hankali a jiya Litinin, da nufin dakile kara tabarbarewar yanayin tsaro. Tun da fari dai daliban jami'ar sun yi boren ne, domin nuna kin jinin abun da suka kira murzunawa dalibai da mahukuntan jami'ar ke yi. Sai dai kuma daga bisani bore ya rikide zuwa tashin hankali, wanda ya haifar da lalata wasu babura da motoci, da gine ginen jami'ar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China