in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana ya jagoranci kaddamar da masana'antar sarrafa kunzugun yara
2018-12-07 09:41:32 cri
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya kaddamar da masana'antar sarrafa kunzugun yara a yankin Bortianor Ngleshie Amanfrom dake kudu maso yammacin birnin Accra.

Shugaba Akufo-Addo wanda ya kaddamar da masana'antar ta 'yan kasuwar Sin a jiya Alhamis, ya bayyana ta da masana'anta irin ta mafi girma a daukacin yankin kudu da hamadar sahara, wadda za ta rika samar da kunzugun yara. Ya ce kafa masana'antar a Ghana manufa ce ta gwamnatin sa, dake da nufin maida Ghana wani dandali na bunkasar masana'antu.

Burin gwamnatin Ghana a cewar shugaban, shi ne aiwatar da manufofin raya zamantakewar al'umma da tattalin arziki. Daga nan sai ya yi kira ga al'ummar kasar, da su ci gaba da hadin gwiwa mai ma'ana da kamfanonin Sinawa masu zuba jari a sassan kasar.

A nasa tsokaci yayin bikin kaddamar da masana'antar, jakadan kasar Sin a kasar Ghana Wang Shiting, ya ce yana da burin yin namijin kokari, wajen ganin an cika dukkanin alkawuran da Sin ta daukarwa Ghana.

Ginin masana'antar dai mallakar kamfanin Sunda International na kasar Sin ya lashe kudi har dalar Amurka miliyan 40. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China