Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatarwa majalisar dokokin kasar kasafin kudin shekarar 2019 da ma manufofin gwamnati game da tattalin arziki. Yana mai cewa, a shekara mai kamawan, gwamnati za ta mayar da hankali wajen gina hanyoyi da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa.
Ya ce, gwamnati za ta inganta zirga-zirgar jama'a da kayayyaki da kayan abinci, da samar da ayyukan yi da dawo da matsayin kasar a matsayin cibiyar jigila, da samar da makamashi da zirga-zirga a yankin.
Ya kuma ba da tabbacin cewa, gwamnati za ta kammala ayyukan da gwamnatin ta gabata ta fara wadanda aka kusa kammalawa. Haka kuma gwamnati za ta hada kai da sassa masu zaman kansu wajen gudanar da wasu ayyuka a sassa dabamn-daban na kasar.(Ibrahim)